‘Yan fanshon jihar Kano sun yi zanga-zanga

30

‘Yan fansho karkashin jagorancin kungiyar kwadago ta kasa NLC a jihar Kano a jiya suka gudanar da zanga-zanga kan rashin biyansu hakkokinsu na ritaya.

Masu zanga-zangar sun koka da rashin biyansu hakkokinsu na tsawon shekaru bayan sun yi ritaya.

Shugaban NLC na jihar, Kabiru Ado Minjibir, wanda ya jagoranci zanga-zangar ya bukaci a biya kashi 17 cikin 100 na kudaden da ma’aikata ke bayarwa duk wata ga asusun fansho.

Kabiru Minjibir ya bayyana cewa zuwa watan Yunin bana, bashin hakkokin wadanda suka yi ritaya jihar ya kai sama da Naira miliyan dubu 36, kuma kashi 17 cikin 100 na kudaden da ba a biya ba, daga kungiyoyin da suka gaza biya, ya kai sama da Naira miliyan dubu 69.

Ya ce adadin hakkokin ‘yan fanshin ya fara taru karkashin gwamnatoci uku daga watan Afrilu 2006 zuwa Agustan bana, karkashin Malam Ibrahim Shekarau, Rabiu Musa Kwankwaso da gwamna mai ci Abdullahi Umar Ganduje.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

fifteen + nine =