Wata cibiya daga Jos ta raba kekunan guragu 120 a Jigawa

21

Wata cibiyar masu bukata ta musamman da ke Jos a Jihar Filato ta ba da tallafin keken guragu ga masu nakasa su 120 a kauyen Babaldu da ke Karamar Hukumar Birnin Kudu a Jihar Jigawa.

Babban Daraktan Cibiyar, Ayuba Gufwan, wanda ya mika kekunan guragun ga wadanda suka ci gajiyar, ya ce sun dauki wannan mataki ne da nufin ganin ba a bar nakasassu a baya ba a cikin al’umma.

Ayuba Gufwan, wanda ya warke daga cutar shan inna, ya shawarci wadanda suka amfana da kada su kalli nakasarsu a matsayin alamun mutuwa, sai dai su dauki nakasar a matsayin kalubalen dake bukatar a shawo kan shi.

Ya kuma bukaci wadanda suka amfana da su yi amfani da keken guragu wajen gudanar da sana’o’i masu ma’ana, kada su shiga barace-barace.

Hakimin kauyen Babaldu, Alhaji Usman Lamido, ya godewa cibiyar bisa wannan karimcin, inda ya ce cibiyar ta tallafa wa nakasassu a kauyen da kekunan guragu sama da 500 a baya.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

20 − 8 =