Shugaban kasa da wasu masu rike da mukaman siyasa zasu samu karin albashi

30

Hukumar raba kudaden shiga da tsara albashi (RMFAC) ta bayyana cewa ta kammala shirye-shiryen fara karin albashin masu rike da mukaman siyasa da manyan ma’aikatan gwamnati da kuma ma’aikatan shari’a a kasar nan.

Wata sanarwa da hukumar ta fitar ta nakalto shugaban hukumar Mohammed Bello Shehu ne ya bayyana hakan a yayin wata ziyarar ban girma da suka kai wa shugaban kungiyar gwamnonin Najeriya Gwamna Aminu Waziri Tambuwal na jihar Sokoto a ofishinsa da ke Abuja.

Sai dai kungiyar kwadago ta Najeriya NLC da wasu masana sun ce sanarwar hukumar ta tayar da hankali duba da cewa mafi karancin albashi na naira dubu 30 ga ma’aikatan gwamnati ba komai ba ne idan aka kwatanta da makudan kudaden da ‘yan siyasa ke karba a matsayin albashi da alawus-alawus.

Wadanda za su ci gajiyar karin albashin sun hada da shugaban kasa, da mataimakin shugaban kasa, da gwamnoni da mataimakansu, da ‘yan majalisa da sauran masu rike da manyan mukaman siyasa.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

20 − 16 =