Mataimakin Shugaban Kasa yace shirye-shiryen tallafawa al’umma da tattalin arzikin zamani da saukaka hanyoyin gudanar da kasuwanci, na daga cikin manyan nasarorin gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari cikin shekaru 7 da suka gabata.
Mataimakin shugaban kasar yayi magana jiya a Abuja yayin taron bibiyar ayyukan ministoci da aka shirya domin auna cigaban da aka samu wajen aiwatar da manufar gwamnati.
A cewar mataimakin shugaban kasar, shirye-shiryen sun nuna cewa abu ne mai yiwuwa a aiwatar da manyan shirye-shirye domin amfanin talakawan Najeriya bisa gaskiya da adalchi.
Yace shirin ciyar da daliban firamaren gwamnati ya na ciyar da ‘yan makaranta kimanin miliyan 10 a fadin kasarnan.
Yemi Osinbajo ya kara da cewa shirye-shiryen tallafin jari ga ‘yan kasuwa da manoma wadanda suka samu lambar yabo, na daga cikin manyan nasarorin gwamnatin.