Matasan NYSC za su maimata shekarar yiwa kasa hidima a Bauchi

34

Ko’odinetan hukumar matasa masu yiwa kada hidima, NYSC, a jihar Bauchi, Namadi Abubakar, a yau ya bayyana cewa masu yiwa kada hidima 4 ‘yan Rukunin C kashin 1 na shekarar 2021, za su maimaita shekarar hidimar su a jihar.

Namadi Abubakar ya bayyana hakan ne a wata hira da ya yi da Kamfanin Dillancin Labarai na kasa a Bauchi a lokacin rabon takardar shaidar sallamar masu yiwa kasa hidima.

Ya ce an hukunta masu yiwa kasa hidima da suka aikata laifuka daban-daban da suka hada da tserewa da kuma rashin zuwa aikinsu.

Namadi Abubakar ya ce za a kara wa wasu masu yiwa kasa hidima su 27 wa’adin yiwa kasa hidima na akalla makonni uku bisa wasu laifuka da suka aikata a shekarar yiwa kasa hidima.

A cewarsa, daga cikin masu yiwa kasa hidima dubu 1 da 151 da aka yaye, biyar daga cikinsu za a ba su lambar yabo ta jiha bisa gagarumin gudunmawar da suka bayar wajen inganta rayuwar al’ummar da suka karbi bakuncinsu.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

9 + 14 =