Majalisar dokokin jihar Kogi a jiya ta gayyaci kamfanin siminti na BUA akan wani fili mai fadin hekta dubu 50 da ya mallaka shekaru 10 da suka gabata amma har yanzu bai biya ba.
‘Yan majalisar sun yi wannan sammacin ne a wani taron jin ra’ayin jama’a na daya daga cikin kwamitocin majalisar na wucin gadi da aka gudanar a wani otal da ke Lokoja, babban birnin jihar, tun bayan da gobara ta kone ginin majalisar a ranar Litinin da ta gabata.
Mataimakin kakakin majalisar, Alfa Momoh-Rabiu, wanda ya karanta sammacin bayan ya saurari mukaddashin babban safiyo na jihar, Salihu Mustapha, ya bayyana kaduwarsa da abinda kamfanin BUA ya yi.
Shugaban kwamitin wucin gadi, Umar Tenimu, ya ce babban laifi ne kamfanin BUA ta rike filin sama da shekaru 10 ba tare da biyan kudin sa ba.
Ya ce a kira kamfanin da ya zo ta bayyana dalilin da ya sa ya ki biyan kudin fili da kuma dalilin da ya sa ta ki biyan diyya ga mutanen da abin ya shafa.
Ya kara da cewa idan kamfanin BUA ta ki biyan kudin filin da kuma biyan diyya ga jama’a, gwamnati za ta kwace takardar shaidar mallakin filin.