Liz Truss ta yi murabus daga mukaminta na firai-ministar birtaniya

33
New Conservative Party leader and Britain's Prime Minister-elect Liz Truss gestures as she delivers a speech at an event to announce the winner of the Conservative Party leadership contest in central London on September 5, 2022. - Truss is the UK's third female prime minister following Theresa May and Margaret Thatcher. The 47-year-old has consistently enjoyed overwhelming support over 42-year-old Sunak in polling of the estimated 200,000 Tory members who were eligible to vote. (Photo by Adrian DENNIS / AFP) (Photo by ADRIAN DENNIS/AFP via Getty Images)

Kasa da watanni biyu bayan da ta hau kujerar firaministar Burtaniya, Liz Truss ta yi murabus daga mukaminta.

Liz Truss ta sanar da murabus din nata ne a yau yayin wata ganawa da manema labarai a wajen titin Downing da ke birnin Landan.

‘Yan majalisar wakilai fiye da goma daga jam’iyyarta ta Conservative sun yi kira da ta yi murabus bisa kalubalen tattalin arzikin da kasar ke fuskanta.

Akalla mambobi biyu na majalisar ministocinta ma sun yi murabus daga mukaminsu.

Liz Truss ta ce ta yi murabus ne saboda ba za ta iya gudanar da aikin da aka zabe ta ba.

Ta ce ta sanar da sarkin Birtaniya, wanda shi ne shugaban kasa, game da murabus din ta a shugabancin jam’iyyar.

Za a gudanar da zaben sabon firaminista a mako mai zuwa kuma za ta ci gaba da kasancewa a kan mukamin har zuwa lokacin.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

three × 1 =