A karshe dai kungiyar malaman jami’o’i (ASUU) ta dakatar da yajin aikin da ta fara a ranar 14 ga watan Fabrairun bana.
Kungiyar ta kawo karshen yajin aikin ne bayan tattaunawa mai zafi da gwamnati, musamman tattaunawar da majalisar wakilai ta jagoranta karkashin shugabancin kakakinta, Honorabul Femi Gbajabiamila.
Rahotannin sun sanar da yadda kungiyar ta ASUU ta fara dogon zaman ganawa bayan tattaunawa da majalisar wakilai ta kasa.
Bayan tattaunawa, shugaban kungiyar malaman jami’o’i (ASUU), Farfesa Emmanuel Osodeke, ya ce kungiyar za ta iya janye yajin aikin da take yi nan da ‘yan kwanaki kalilan.
Ko da yake har yanzu ASUU ba ta bayyana matakin janye yajin aikin ba a hukumance, wani dan kungiyar daga Jami’ar Legas ya tabbatar da janye yajin aikin ga manema labarai a safiyar yau.