Kotu ta daure dattijon da ya lalata yarinya karama a Jigawa

87

Wata babbar kotun jihar Jigawa dake zamanta a Dutse ta yankewa wani dattijo mai suna Dayyabu Madaki dan shekara 60 hukuncin daurin rai da rai bisa samunsa da laifin lalata wata yarinya.

An gurfanar da wanda ake tuhuma a gaban kotu watannin baya da laifin yin jan hankalin wata yarinya ‘yar shekara 9 zuwa gidansa tare da yin lalata da ita da karfi a kauyen Doro da ke karamar hukumar Jahun.

Wanda ake tuhumar ya musanta aikata laifin da ake tuhumarsa.

Sai dai lauyan mai gabatar da kara, ya gabatar da shaidu ciki har da bayanin ‘yan sanda na wanda ake kara da kuma rahoton likita don tabbatar da hujjarsa.

Ya ce laifin fyaden yana da hukuncin daurin rai da rai idan aka tabbatar da laifi.

Da yake yanke hukuncin, Alkalin Kotun, Mai shari’a Sambo ya ce Lauyan masu kara ya tabbatar da laifin ba tare da wata shakka ba, don haka ta yanke wa wanda ake tuhuma hukuncin daurin rai da rai.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

6 − three =