INEC ta gayyaci kungiyoyin kasa da kasa domin sanya ido a zaben 2023

37

Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa, INEC, ta gayyaci kungiyoyin kasa da kasa a fadin duniya da su zo su sanya ido a zaben Najeriya na 2023.

Shugaban hukumar ta INEC Mahmood Yakubu ya yi wannan kiran ne a lokacin da ya karbi bakuncin tawagar kungiyar raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afirka, ECOWAS, mai fafutukar gano gaskiyar zabe a Najeriya, a hedikwatar hukumar jiya a Abuja.

Kungiyar ta samu jagorancin tsohon shugaban hukumar zaben kasar Ghana, Kwadwo Afari-Gyan.

Shugaban na INEC ya bayyana cewa hakan na nuni ne da dabi’ar hukumar na yin abu a faifai da kuma al’adar hukumar na karbar masu sa ido na kasa da kasa.

Kuma ya tabbatar wa kungiyar ta ECOWAS cewa za a yi amfani da fasahar zamani a zabukan Najeriya na 2023.

Da yake magana a madadin tawagar, Remi Ajibewa, ya ce sun zo Najeriya ne domin gano gaskiyar zabukan kasar a shekarar 2023 kamar yadda dokokin ECOWAS na 2021 suka tanadar domin sa ido a zabukan Najeriya.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

twelve − 10 =