Hisbah ta kama motoci uku makare da kwalaben giya a Kano

26

Hukumar Hisbah a jihar Kano ta ce ta kama wasu motoci uku makare da kwalaben giya guda dubu 5 da 800.

Babban Kwamandan Hukumar Hisbah, Haruna Ibn-Sina ne ya bayyana haka jiya a Kano yayin da yake duba motocin da aka kama a ofishin Hisbah.

Kakakin hukumar, Lawan Fagge, ya bayyana cewa an kama motocin uku ne a ranar Lahadi.

Motocin dai sun hada da mota kirar Mercedes Benz, wacce ke dauke da kwalaben giya dubu 1 da 800; sai mota kirar Sienna dauke da kwalaben giya dubu 3 sai Golf Volkswagen dauke da kwalaben giya dubu 1.

Lawan Fagge ya bayyana cewa Haruna Ibn-Sina ya yabawa sashin dakile kayan maye bisa kokarinsu na ganin an daina shan barasa da muggan kwayoyi a jihar.

Ya kuma ba da tabbacin cewa hukumar ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen ganin ta tsaftace jihar Kano daga duk wani nau’i na munanan dabi’u musamman safarar miyagun kwayoyi da ta’ammali da miyagun kwayoyi.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

12 − 2 =