Har yanzu ba a kamo fursunoni sama da 400 da suka tsere daga Kuje ba

26

Fiye da fursunoni 422 da suka tsere daga gidan yarin Kuje dake Abuja, a ranar 5 ga watan Yuli bana, har yanzu ba a kama su ba.

Sky Daily Hausa ta cewa fursunoni 879 da suka hada da manyan mayakan Boko Haram 64 ne suka tsere daga gidan yarin a lokacin da aka fasa gidan yarin.

Kakakin hukumar kula da gidajen gyaran da’a ta kasa, Umar Abubakar, ya ce mutane biyar da suka hada da jami’in tsaron civil defence da kuma wasu fursunoni hudu sun mutu a harin.

Sa’o’i kadan bayan harin, kungiyar ISWAP ta dauki alhakin kai harin.

An ruwaito cewa kwamitin majalisar wakilai mai kula da gidajen gyaran da’a ya ce hukumar gidajen gyaran da’a ta kasa ta sake cafke fursunoni 421 amma har yanzu ba a kama 454 ba.

Rahotanni daga kafafen yada labarai na cewa, a tsakanin ranar 15 ga watan Yuli zuwa 3 ga watan Oktoban bana, an sake kama a kalla fursunoni 32 daga cikin 454 da suka tsere.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

12 + fourteen =