Gwamnatin Jigawa ta samar da injinan ruwa a Nijar

80

Gwamnatin jihar Jigawa ta samar da injinan samar da ruwa masu amfani da guguwa da hasken rana guda biyu a jihar Damagaram a jamhuriyar Nijar.

Gwamna Muhammad Badaru Abubakar ne ya bayyana haka a lokacin da yake mika injinan ga gwamnan Damagaram, Alhaji Lawwali Amadi.

Gwamna Badaru Abubakar wanda ya samu wakilcin babban mai taimaka masa na musamman kan harkokin noma, Alhaji Muhammad Idris Danzomo, ya ce matakin ya cika alkawarin da ya dauka a ziyarar da ya kai jihar.

Ya ce samar da injinan zai inganta alakar da ke tsakanin manoma da makiyaya a jihohin biyu.

Da yake mayar da martani, Gwamna Lawwali Amadi na Damagaram ya yabawa Gwamna Badaru Abubakar bisa samar da injinan wadanda za su taimaka matuka wajen kyautata alaka a tsakanin jihohin biyu.

Daga baya gwamnonin biyu sun rattaba hannu kan wata yarjejeniyar fahimtar juna.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

two + 16 =