Gwamnatin Jigawa ta raba N700m ga marasa galihu

16

Gwamnatin Jihar Jigawa ta raba kudi fiye da naira miliyan 700 karkashin shirin NG CARES a fadin jihar.

Gwamna Muhammad Badaru Abubakar ya bayyana haka lokacin kaddamar da shirin fadama kashi na biyu a hukumar bunkasa aikin gona da raya karkara da aka gudanar a Dutse.

Muhammad Badaru Abubakar wanda ya samu wakilcin mataimakin sa Malam Umar Namadi, ya ce an raba kudaden ne domin inganta rayuwar marasa galihu karkashin shirin tallafawa rayuwar masu karamin karfi na kasa.

Ya ce gwamnati za ta ci gaba da marawa shirye-shiryen baya domin cimma burin da aka sanya a gaba na farfadowa daga mawuyacin hali da annobar korona ta jefa duniya a ciki.

A nasa jawabin, kwamishina mai kula da ma’aikatar aikin gona, Auwalu Danladi Sankara ya ce raba kayayyakin aikin ga manoma wadanda za su taimaka wajen samar da abinci da kuma bunkasa tattalin arziki.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

9 + 14 =