Gwamnatin Jigawa ta kafa kwamitocin tallafawa wadanda ambaliya ta shafa

67

Gwamnatin jihar Jigawa ta kaddamar da wasu kwamitoci guda biyu masu karfi domin dakile illolin ambaliyar ruwa a jihar.

Gwamnan jihar, Muhammad Badaru Abubakar ya kaddamar da kwamitocin yau a gidan gwamnati dake Dutse babban birnin jihar.

Kwamitocin biyu sun hada da kwamitin jihar kan tantance iftila’in ambaliyar ruwa, da tara kudade, da kuma kwamitin kwararru kan dakile ambaliyar ruwa.

A cewar gwamnan, kwamitin tattara kudade na da nauyin tattara kudade da kuma raba kayan agaji ga wadanda ambaliyar ruwa ta shafa a fadin jihar.

Ya kara da cewa kwamitin kwararru kan dakile ambaliyar ruwa na samar da mafita ta din-din-din kan matsalar ambaliyar ruwa da ta addabi jihar Jigawa.

Ya zuwa yanzu gwamnatin jihar ta samu sama da naira miliyan 500 na tallafin ambaliyar ruwa daga gwamnatin tarayya, da kungiyoyin bayar da tallafi da kuma daidaikun mutane masu hannu da shuni.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

14 − 1 =