Gwamnatin kasar Canada ta sanar da tallafin kudi dala miliyan uku, kwatankwacin naira miliyan dubu 1 da miliyan 300 ga gwamnatin jihar Bauchi domin inganta shigar da mata a harkokin kiwon lafiya.
Shugaban ofishin asusun yara na majalisar dinkin duniya (UNICEF) a Bauchi, Tushar Rane, shine ya sanar da haka lokacin da gamayyar tawagar UNICEF da gwamnatin Canada suka ziyarci gwamnan jihar Bauchi, Bala Muhammad, jiya a Bauchi.
Yace manufar tallafin kudaden shine bawa mata sana’a domin basu damar shiga a dama da su wajen samar da kiwon lafiya tare da cin gajiyarsa.
Tunda farko, shugaban sashen cigaba da hadin kai na ofishin jakadancin Canada a Najeriya, Djifa Ahado, ya bayyana hadin kai da gwamnatin jihar a matsayin daya daga cikin manyan nasarori.
Da yake mayar da martani, Gwamna Bala Mohammed ya bayyana godiya ga gwamnatin Canada bisa tallafin da take bayarwa jihar.