Gwamnatin tarayya ta ayyana ranar Litinin mai zuwa, 10 ga watan Oktoba, a matsayin ranar hutu domin murnar zagayowar ranar haihuwar fiyayyen halitta Annabi Muhammad SAW.
Babban sakataren ma’aikatar harkokin cikin gida, Shu’aib Belgore ne ya bayyana hakan a wata sanarwa jiya a Abuja.
A cewarsa, ministan harkokin cikin gida, Rauf Aregbesola, wanda ya bayyana hutun a madadin gwamnatin tarayya, ya taya daukacin al’ummar musulmi na gida da kuma na kasashen waje murnar mauludi.
Ministan ya hori dukkan ‘yan Najeriya da su yi koyi da soyayya, hakuri, juriya da nagarta wadanda su ne kyawawan dabi’un da Manzon Allah ya yi misali da su.
Ya ce yin hakan zai tabbatar da zaman lafiya da tsaro da kwanciyar hankali a kasar.
Rauf Aregbesola ya bukaci ‘yan Najeriya musamman musulmi da su guji tashin hankali da rashin bin doka da oda da sauran ayyukan ta’addanci.