Gwamnan jihar Jigawa Muhammad Badaru Abubukar ya amince da nadin Dr Atiku Hafizu Ringim a matsayin mai bashi shawara kan kiwon lafiya.
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa a jiya da sakataren gwamnatin jiha Alhaji Adamu Abdulkadir Fanini ya sanyawa hannu.
Haka kuma gwamnan ya amince da nadin Ambassada Usman Inuwa Dutse a matsayin babban mataimaki na musamman ga gwamna kan tsaftar mahalli da kuma Hassan Shakara Hadejia a matsayin babban mataimaki na musamman ga gwamna kan samar da ruwan sha a yankunan karkara.
Sanarwar ta kara da cewa dukkan nade-naden sun fara aiki nan take.