El-Rufa’i ya gabatar da kasafin kudin N370bn ga majalisa

25

Gwamna Nasir El-Rufa’i na jihar Kaduna a jiya ya gabatar da daftarin kasafin kudin badi na naira miliyan dubu 370 ga majalisar dokokin jihar.

Kasafin kudin ya dace da tsarin kasafin kudin gwamnatinsa na kashi 60 cikin 100 na manyan ayyuka da kashi 40 cikin 100 na kudaden gudanar da gwamnati.

Gwamnan yace kasafin kudin 2023 ya kunshi kudi naira miliyan dubu 370 da miliyan 330, wanda ya haura kasafin kudin bana na naira miliyan dubu 303 da miliyan 990 da kashi 21.82 cikin 100.

Nasir El-Rufa’i yace an ware naira miliyan dubu 242 da miliyan 210 domin manyan ayyuka, yayin da aka ware naira miliyan dubu 127 da miliyan 700 domin gudanar da gwamnati.

Gwamnan ya kara da cewa kasafin kudin na badi ya bayar da fifiko ga manufar gwamnati ta gina rayuwar al’umma.

A cewarsa, ware kashi 29 cikin 100 ga bangaren ilimi da kashi 16.05 cikin 100 ga bangaren lafiya, ‘yar manuniya ce bisa ga jajircewar gwamnatinsa wajen gina rayuwar al’umma.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

3 × 3 =