CBN ya sayar da bankin Polaris

75

Babban bankin kasa, CBN, ya sanar da sayar da bankin Polaris ga wani sabon Kamfani mai saka hannun jari mai suna Strategic Capital Investment.

Wata sanarwa da Daraktan Sadarwa na CBN, Osita Nwanisobi, ya sanyawa hannu, kuma aka wallafa a shafin intanet na CBN a jiya, ta ce an kammala cinikin ne bayan yarjejeniyar sayen hannun jari domin sayar da kashi 100 na hannun jarin bankin.

Bankin Polaris dai yana aiki ne a matsayin bankin wucin gadi tun shekarar 2018 lokacin da CBN ya shiga tsakani inda ya kwace lasisin tsohon bankin Skye.

Babban bankin na CBN ya kuma kafa bankin Polaris domin karbar kadarorinsa da wasu basussuka.

Sanarwar ta ce Strategic Capital Investment ya biya kudin da ya kai naira miliyan dubu 50 domin sayen kashi 100 na hannun jarin bankin Polaris.

Sanarwar ta ci gaba da cewa, an kuma amince da sharuddan yarjejeniyar da suka hada da biyan dukkan kudaden da suka kai Naira tiriliyan 1 da miliyan dubu 305.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

fourteen − twelve =