Buhari ya taya Gowon murnar cikarsa shekaru 88

19

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari a jiya ya taya murna ga tsohon shugaban kasa, Janar Yakubu Gowon, mai ritaya, bias cikarsa shekaru 88 a duniya.

Shugaba Buhari, kamar yadda yazo a wata sanarwa daga kakakinsa, Femi Adesina, ya taya murna ga uban kasar wanda kalamansa da addu’o’insa da sadaukarwarsa ke cigaba da haifarwa da kasarnan da mai ido.

Yayi nuni da jajircewar tsohon shugaban kasar wajen neman hadin kai, zaman lafiya da cigaban Najeriya, Afrika ta Yamma da ma nahiyar Afrika, inda yake taka muhimmiyar ruwa wajen cigaban tattalin arziki da walwalar jama’ar kasarnan, tare da assasa kungiyar cigaban kasashen Afrika ta Yamma (ECOWAS).

Yace dayawa daga cikin shekarun Yakubu Gowon, da suka hada da shekarunsa na aiki a matsayin soja, ya sadaukar da su ne wajen gina kasa da kudure-kudure irinsu kirkirar jihohi, da samar da hukumar matasa masu yiwa kasa hidima NYSC.

Shugaban kasar yayi addu’ar karin lafiya, karfin jiki da tsawon rayuwa ga Yakubu Gowon tare da iyalinsa.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

13 − 12 =