Buhari ya gana da fasinjojin jirgin kasan da aka saki

33

Shugaban kasa Muhammadu Buhari a yau ya gana da fasinjoji 23 da aka sako wadanda aka sace a harin jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna a asibitin makarantar horas da sojoji ta NDA a Kaduna.

Mai taimakawa shugaban kasa kan harkokin yada labarai, Garba Shehu, ya tabbatar da hakan a wata sanarwa yau a Abuja.

A cewar hadimin shugaban kasar, shugaba Buhari ya kai ziyarar bazata zuwa asibitin domin duba wadanda harin jirgin kasa ya rutsa da su bayan kaddamar da sojojin da aka yaye a NDA, aji na 69, a Afaka, jihar Kaduna.

Mambobin kwamatin karta kwana na babban hafsan tsaron kasa karkashin jagorancin Manjo Janar Usman Abdulkadir mai ritaya, wadanda suka taimaka wajen sakin wadanda harin jirgin kasan ya rutsa da su, sun hallara a asibitin.

Sauran ‘yan kwamitin sun hada da Manjo Janar Adamu Jalingo mai ritaya da Birgediya Janar Abubakar Saad mai ritaya da Dokta Murtala Rufa’i da Ibrahim Abdullahi da Ambasada Ahmed Magaji da Farfesa Yusuf Usman, sakataren kwamitin.

Tun da farko babban hafsan hafsoshin tsaron kasa Janar Leo Irabor ya gabatar da mambobin kwamitin ga shugaban kasa.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

three × 1 =