Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya umarci ministan albarkatun ruwa da ya jagoranci tare da hada kai da ma’aikatun da suka kamata da gwamnatocin jihoshi wajen samar da wani cikakken kundin aikin magance annobar ambaliyar ruwa a Najeriya.
Hadimin shugaban kasa, Garba Shehu, cikin wata sanarwa da ya fitar jiya a Abuja, ya ambaci sunayen ma’aikatun da abin ya shafa da suka hada da ma’aikatar muhalli da ma’aiktar sufuri.
Garba Shehu yace umarnin shugaban kasar, wanda aka aikawa ministan cikin wata wasika dauke da sa hannun shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa, Farfesa Ibrahim Gambari, yace za a aika masa da kundin cikin kwanaki 90 masu zuwa.
A cewar hadimin na shugaban kasa, Shugaba Buhari yana samun rahotannin halin da ake ciki akai-akai dangane da ambaliyar ruwa a kasarnan.
Ya bayar da labarin cewa Shugaban Kasar ya kara jaddada aniyarsa ta magance kalubalen da annobar ta haifar a kasarnan.
A wani labarin mai alaka da wannan, Shugaban Kasa Muhammadu Buhari yace tuni Najeriya ta fara fuskantar illar sauyin yanayi kamar yadda ake gani a ambaliyar ruwa a sassa daban-daban na kasarnan da kuma kwarorowar hamada daga Arewacin kasarnan.
Kakakin shugaban kasa, Femi Adesina, cikin wata sanarwa yace shugaban kasar ya sanar da hakan yayin ganawar da yayi da tsohon sakatare janar na majalisar dinkin duniyar, Ban Ki-Moon.
An gudanar da zaman ganawar a wajen taro farko kan kiwon lafiya na bana, yau a birnin Seoul na kasar Koriya ta Kudu.
Shugaban kasar ya bayyana farincikinsa bisa hadin kan dake akwai tsakanin kasarsa da Koriya, musamman a bangarorin samar da makamashi, inda ya bada misali da yadda Najeriya ke fitar da gas zuwa kasar ta Koriya.
A nasa bangaren, tsohon sakatare janar na majalisar ta dinkin duniyar, wanda kuma shine shugaban gidauniyar Ban Ki-Moon kuma babban mai fafutukar magance sauyin yanayi, ya jajantawa shugaba Buhari bisa iftila’in ambaliyar ruwa a Najeriya.