Bankin raya Musulunchi zai ba wa Najeriya N778bn

56

Shugaban Bankin Raya Musulunci Dr. Mohamed Suleiman Aljasser, ya ce adadin kudaden da bankin ke baiwa Najeriya ya kai dala miliyan dubu 1 da miliyan 800, kwatankwacin sama da naira miliyan dubu 788.

Ya bayyana hakan ne a jiya a yayin rattaba hannu kan yarjejeniyar samar da asibiti a Kaduna mai gadaje 300 da kuma yarjejeniyar fahimtar juna tsakanin bankin da hukumar bunkasa zuba jari ta Najeriya a hedikwatar ma’aikatar kudi, kasafin kudi da tsare-tsaren kasa dake Abuja.

Ya ce bankin ci gaban Musulunci ya himmatu wajen kara zuba jari a Najeriya musamman a fannin noma.

Shugaban bankin ya yabawa gwamnatin tarayya ta Najeriya kan yadda ta kara mayar da hankali a fannin tattalin arzikin kasar tare da yin alkawarin baiwa bankin goyon baya a yunkurin da yake yi na bunkasa tattalin arziki.

Dokta Aljasser ya kuma ce bankin ci gaban Musulunci yana son ci gaba da kulla alaka da Najeriya kan muhimman batutuwan da suka sa gaba kamar su tattalin arziki da zamantakewa.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

12 − 2 =