An raunata mutane da lalata motoci a rikicin APC a Jigawa

375

Akalla mutane hudu ne suka samu raunuka daban-daban kuma aka lalata wasu motoci a Dutse, babban birnin jihar Jigawa, yayin da wasu bangarori biyu na jam’iyyar APC mai mulki suka yi arangama a jihar.

Rikicin dai ya faru ne a jiya da rana a yayin taron gangamin goyon bayan dan takarar gwamna na jam’iyyar a jihar.

Rahotanni sun nuna cewa ‘ya’yan jam’iyyar APC a karkashin kungiyar Matasan Danmodi, sun shirya wani gangamin siyasa domin nuna goyon bayansu ga dan takarar wanda kuma shi ne mataimakin gwamnan jihar mai ci Alhaji Umar Namadi Danmodi a Dutse.

Da yake tabbatar da rikicin, jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Jigawa, DSP Lawal Shiisu Adam, ya ce ‘yan sanda sun yi gaggawar shiga rikicin da ya barke tsakanin bangarorin biyu.

Ya ce jami’an ‘yan sanda sun yi gaggawar shiga tsakani ta hanyar tarwatsa su kuma tuni aka samu zaman lafiya.

Kokarin jin ta bakin wadanda suka shirya gangamin ya ci tura har zuwa lokacin da ake hada wannan rahoto.

Sharhi 1

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

three + nine =