An kashe mutane 37 a wani hari a cibiyar renon yara a Thailand

34

Wani tsohon dan sanda ya kashe akalla mutane 37, yawancinsu kananan yara, a wani harin bindiga da wuka da ya kai a wata cibiyar kula da yara da ke arewa maso gabashin kasar Thailand.

‘Yan sanda sun ce daga nan ne maharin ya kashe kansa da iyalansa bayan an baza komar nemansa bayan harin.

Yan sanda sun ce yara da manya na daga cikin wadanda aka kashe a cibiyar renon yaran kuma maharin ya harbe su tare da caka musu wuka kafin ya gudu daga wajen.

‘Yan sandan sun ce an kori tsohon dan sandan mai shekaru 34 daga aiki a watan Yuni saboda amfani da miyagun kwayoyi kuma ba a san ko yana da dalilinsa na kai harin.

Akalla yara 22 na daga cikin wadanda suka mutu a wannan gagarumin harin. An farwa wasu ‘yan kasa da shekaru biyu a lokacin da suke barci kuma an kai mutane goma 12 da suka jikkata zuwa asibiti.

Shugaban cibiyar ta ce dan maharin yana halartar cibiyar amma ya kai wata daya bai je ba.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

seventeen + seven =