An bai wa ministoci wa’adin kammala manyan ayyukan Buhari

20

Sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha, ya baiwa ministocin wa’adi domin tabbatar da kammala manyan ayyukan da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya assasa kafin karshen gwamnatin sa.

Boss Mustapha ya bayar da wannan umarni ne a taron bibiyar ayyukan ministoci karo na 3, wanda ofishin sakataren gwamnatin tarayya ya shirya wa ministoci da manyan sakatarori da manyan jami’an gwamnati, jiya a Abuja.

Taron na kwanaki 2 wanda aka shirya da nufin samar da sabbin bayanai game da matsayin kudirori, shirye-shirye da ayyukan gwamnati, domin shiryawa mambobin majalisar ministocin da za a nada nan gaba.

An kuma shirya taron domin domin samar da hanyoyin da za a tabbatar gwamnati ta kammala ayyukan da ta fi bawa muhimmanci tsakanin shekarar 2019 zuwa 2023.

Boss Mustapha taron na bana shi ne karo na 4 kuma na karshe a jerin tarurrukan shugaban kasa da aka shirya a wa’adi na biyu na mulkin shugaban kasa Muhammadu Buhari.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

nine − four =