Ambaliya: UNICEF ya bayar da tallafin N230.7m a Jigawa

83

Asusun kula da kananan yara na Majalisar Dinkin Duniya, UNICEF ya ba gwamnatin jihar Jigawa gudummawar Tallafin da ya kai Naira miliyan 230 da dubu 700 domin rabawa wadanda ambaliyar ruwa ta shafa a jihar.

Shugabar ofishin UNICEF reshen Kano, Rahama Farah ce ta bayyana haka a lokacin da ta gabatar da tallafin ga mataimakin gwamnan jihar, Alhaji Umar Namadi.

Rahama Farah wacce Babban Manajan Ilimi na UNICEF, Michael Banda, ya wakilta, ta ce matakin ya biyo bayan tantance sansanonin ‘yan gudun hijirar ne inda wadanda ambaliyar ruwa ta shafa ke samun matsuguni, a daukacin kananan hukumomin jihar.

Tallafin ya kasance a fannonin Ilimi, Abinci, Ruwan Sha, Tsaftar muhalli da Tsaftar jiki, da sauransu.

Da yake mayar da martani, Mataimakin Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi ya gode wa asusun bisa wannan karimcin inda ya ce za a yi amfani da tallafin kamar yadda ya kamata.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

four × 5 =