Ambaliya: NEMA ta raba kayan tallafi a Jigawa

55

Hukumar bada agajin gaggawa ta kasa NEMA, ta bada tallafin kayayyaki na miliyoyin naira ga mutanen da suka gamu da iftila’in ambaliyar ruwa a yankin karamar hukumar Auyo.

Daraktan hukumar mai kula da jihohin Kano da Jigawa, Dokta Nura Abdullahi, ya mika kayayyakin ga shugaban karamar hukumar domin rabawa wadanda ambaliyar ta shafa.

Daraktan wanda ya sami wakilcin daya daga cikin jami’an hukumar, Hassan Abdulkadir, ya ce kayayyakin sun hada da kananan buhunan shinkafa da na wake masu nauyin kilogiram goma-goma guda dubu dai-dai da buhunan masara dubu 4 da tabarmun leda guda 100 da jarkokin man girki da kuma katan 100 na magi.

Sauran kayayyakin sune katan 100 na timatirin gwangwani da gidan sauro da kayayyakin sawa na yara 150 da na mata guda dubu 1 da kuma bandiran yadi 150.

Da yake amsar kayayyakin shugaban karamar hukumar ta Auyo Muhammad Ahmed Sani ya yabawa hukumar tare da bada tabbacin raba kayayyakin ga wadanda ambaliyar ruwan ta shafa.

A wani labarin kuma, Bankin Duniya da hadin gwiwar Gwamnatin Tarayya sun samar da awakin kiwo 600 ga mata 200 a yankin karamar hukumar Auyo karkashin shirin bada rance na J-Care domin rage radadin Annobar Korona.

Shugaban kula da shirin a Jihar Jigawa, Dokta Ahmed Zubairu ya sanar da haka lokacin raba rancen awakin a Garin Auyo.

Ya ce kowace mace zata sami awaki uku, inda zata biya rancen da awaki uku bayan shekaru uku domin sake rabawa wasu matan su amfana.

A nasa jawabin, shugaban Karamar Hukumar ta Auyo, Alhaji Muhammad Ahmed Sani ya yabawa bankin duniya bisa bullo da shirin, inda ya bada tabbacin majalisar karamar hukumar na yin duk abin da ya dace domin samun nasarar shirin.

A nasu bangaren, matan da suka amfana da rancen awakin sun yi alkawarin dawo da rancen akan lokaci kamar yadda aka tsara.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

twelve − eight =