Akalla mutane 150 aka kashe cikin kwanaki biyu na rikici a Sudan

35

Akalla mutane 150 ne aka ruwaito an kashe a rikicin kabilanci a cikin kwanaki biyun da suka gabata a jihar Blue Nile da ke kudancin kasar Sudan.

An ce fadan shi ne mafi muni a watannin baya-bayan nan.

Rikicin dai ya barke ne a makon da ya gabata a tsakanin kabilun da ke gaba da juna bayan rikicin filaye da ya yi sanadiyar mutuwar mutane fiye da goma.

An sanya dokar hana fita ta dare domin shawo kan tashin hankalin.

Majalisar Dinkin Duniya ta fada a jiya cewa ta firgita saboda tashe-tashen hankula a Lagawa da kuma sake barkewar rikici a yankin Blue Nile.

Tawagar Majalisar Dinkin Duniya a Sudan a cikin wata sanarwa da ta fitar ta ce zaman lafiya mai dorewa ba zai yiwu ba matukar babu tsayayyar gwamnati mai cikakken iko da ke ba da fifiko kan bukatun al’umma, ciki har da tsaro da magance rikici.

Sudan dai na fama da tashe-tashen hankula na siyasa da rikice-rikice tun bayan juyin mulkin da sojoji suka yi a bara.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

19 − ten =