A yau ne za a rantsar da shugaban kasar Angola João Lourenço a wa’adi na biyu bayan da ya lashe zabe mafi tsauri a kasar.
Jam’iyyarsa ce ke mulkin kasar tun bayan samun ‘yancin kai daga kasar Portugal a shekarar 1975.
João Lourenço ya bayyana sakamakon zaben a matsayin kuri’ar amincewa da mulkinsa.
Sai dai shugaban kasar zai sha wahala wajen shawo kan matasa masu neman sauye-sauyen da ke tasiri ga ingancin rayuwarsu.
Shugaban kasar mai shekaru 68 a duniya ya yi yakin neman zabe a kan daukar kakkarfan matakin yaki da cin hanci da rashawa.