‘Yan takarar shugaban kasa sun rattaba hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya

57

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bukaci ‘yan siyasa a zaben 2023 da su fifita Najeriya a gaba fiye da muradun yankinsu, gabanin babban zabe na 2023.

Shugaba Buhari ya yi wannan kiran ne a cikin sakon fatan alheri da ya aika wajen rattaba hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya ta kasa da ‘yan takarar shugaban kasa na jam’iyyun siyasa a zaben 2023 suka yi, yau a Abuja.

Ya bukaci kafafen yada labarai da su guji labaran karya da kuma nuna jajircewa wajen gudanar da yakin neman zabe na gaskiya da adalci da kuma sahihin zabe.

Ya ce a matsayinsa na shugaban kasa, ya sha nanata kudurin sa na ganin an gudanar da zabe cikin lumana da kuma gaskiya.

Shugaba Buhari ya yabawa kwamitin zaman lafiya na kasa karkashin jagorancin Janar Abdulsalami Abubakar mai ritaya, bisa jajircewar da suka yi na tallafawa zabuka a Najeriya cikin kwanciyar hankali.

Ya ce abin da kwamitin ke yi a tsawon shekaru, ya yi daidai da imaninsa cewa Najeriya na bukatar zaman lafiya don samun sahihin zabe.

A halin da ake ciki, ‘yan takarar shugaban kasa na dukkanin jam’iyyun siyasa sun rattaba hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya tare da sadaukar da kansu don yakin neman zabe cikin lumana na zaben 2023.

Dukkanin ‘yan takara da shugabannin jam’iyyunsu na kasa sun sanya hannu kan yarjejeniyar da kwamitin zaman lafiya na kasa ya shirya yau a Abuja.

Wasu daga cikin ‘yan takarar da suka sanya hannu kan yarjejeniyar sun hada da Atiku Abubakar na jam’iyyar PDP, Peter Obi na jam’iyyar Labour, da Rabi’u Musa Kwankwaso na jam’iyyar NNPPP.

Sauran sun hada da Omoyele Sowore na jam’iyyar AAC, Hamzat Al-Mustapha na jam’iyyar AA, Sunday Adenuga na jam’iyyar Boot da kuma mace daya tilo a takarar, Chichi Ojei ta jam’iyyar APM.

Christoper Imumolen na Jam’iyyar Accord; Yabagi Sani na jam’iyyar ADP, Dumebi Kachikwu na jam’iyyar ADC, da Dan Nwanyanwu na jam’iyyar ZLP suma sun sanya hannu kan yarjejeniyar.

Dan takarar jam’iyyar APC mai mulki, Bola Tinubu, ya samu wakilcin abokin takararsa na mataimaki, Kashim Shettima.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

twenty + 13 =