Uganda ta tabbatar da sabuwar barkewar Ebola

32

Wani matashi dan shekaru 24 da ya kamu da cutar Ebola ya mutu a tsakiyar kasar Uganda a wani sabon barkewar cutar da jami’an kiwon lafiya suka tabbatar.

Ministan lafiyan kasar ya shaidawa manema labarai cewa wanda ya kamu da cutar ya nuna alamun cutar kafin ya mutu.

Ya kasance mazaunin kauyen Ngabano da ke gundumar Mubende mai tazarar kilomita 147 daga Kampala babban birnin kasar.

Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) a cikin wata sanarwa da ta fitar ta ce Cibiyar Bincike Kan Kwayoyin Cuta ta kasar Uganda ta tabbatar da bullar wani nau’in cutar mai lakabin Sudan da ba a fiye gani ba sosai.

Ta ce mutane takwas da ake zargi da alamun cutar suna samun kulawa, kuma tana tura ma’aikata zuwa yankin da abin ya shafa.

Kasar dake gabashin Afirka ta bayar da rahoton bullar nau’in cutar a shekarar 2012.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

11 − 9 =