Shugaban hukumar ‘yansanda yayi murabus

139

Shugaban hukumar ‘yansanda Musiliu Smith ya yi murabus daga mukaminsa.

Musliu Smith, wanda tsohon sufeto janar na ‘yan sanda ne, ya fuskanci zarge-zargen cin hanci da rashawa da rashin jituwa da Sufeto Janar na ‘yan sanda kan daukar kananan ‘yan sanda aiki.

An bayyana yadda wata kwamishiniyar hukumar, Naja’atu Muhammad ta rubuta korafi kan hukumar ‘yan sanda zuwa hukumar EFCC, inda ta yi zargin badakalar kwangilar miliyoyin naira, almubazzaranci da dukiyar al’umma da kuma rashin bin ka’ida wajen tafiyar da hukumar.

A cikin takardar korafin mai dauke da kwanan watan 29 ga watan Yuni bana, Naja’atu Muhammad, wacce ke wakiltar Arewa maso Yamma a hukumar, ta yi zargin cewa shugaban hukumar ya bayar da kwangiloli na bogi ba tare da bin ka’ida ba.

Ko da yake har yanzu hukumar ba ta bayar da sanarwar a hukumance ba, wani kwamishina a hukumar ya tabbatar da cewa an bukaci Misliu Smith da ya mika mulki ga alkalin kotun koli mai ritaya, Clara Ogunbiyi, a matsayin wanda zai maye gurbinsa.

Kakakin hukumar, Ikechukwu Ani, shi ma ya tabbatar da murabus din, sai dai ya ce shugaban ya yi murabus ne bisa dalilai na rashin lafiya.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

18 + eleven =