Sarauniyar Ingila Elizabeth ta rasu

94

Sarauniyar Ingila Elizabeth ta biyu, wadda ta fi dadewa a kan karagar mulki ta rasu a Balmoral tana da shekara 96 a duniya, bayan ta shafe shekaru 70 tana sarauta.

Tun dazu iyalinta suka taru a gidanta na Scotland bayan damuwa game da lafiyarta.

Sarauniyar ta hau kan karagar mulki a shekarar 1952 kuma ta ga babban canji na zamantakewa.

Bayan mutuwarta, babban danta Charles, tsohon Yariman Wales, zai jagoranci kasar cikin makoki a matsayin sabon sarki kuma jagoran kasashe 14 na kungiyar kasashen rainon Ingila ta Commonwealth.

Duk ‘ya’yan marigayiya sarauniyar sun isa birnin Balmoral, dake kusa da birnin Aberdeen, bayan likitoci sun sanya sarauniyar a karkashin kulawa ta musamman.

Jikanta, Yarima William, yana can, inda dan uwansa, Yarima Harry, yake kan hanya.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

three × 4 =