Ruftawar gini ya jawo mutuwar yara 3 a Jigawa

100

Yara 3 ne aka ruwaito sun mutu bayan ruftawar gini sakamakon ruwan sama da aka shafe sa’o’i ana yi a kauyen Jigawar Tsada da ke karamar hukumar Dutse a jihar Jigawa.

Yaran da suka mutu sun hada da Farida Idi ‘yar shekara shida da Mariya Idi ‘yar shekara uku da kuma Bilkisu Yahya ‘yar watanni 18 da haihuwa dukkansu ‘yan unguwar Yakasai a kauyen Jigawar Tsada.

A wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Jigawa, Lawan Shiisu Adam ya fitar, ya ce wadanda abin ya shafa sun mutu nan take.

Shiisu Adam ya ce bayan samun rahoton faruwar lamarin, ‘yan sanda sun garzaya zuwa wajen da lamarin ya faru, inda suka kwashe yaran tare da garzaya da su babban asibitin Dutse inda likitan da ke bakin aiki ya tabbatar da mutuwar su.

Ya kara da cewa an dauki hoton gawarwakin kuma an mika su ga ‘yan uwan yaran domin yi musu jana’iza.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

seventeen + four =