Hukumar shirya jarabawar ta kasa (NECO) a yau ta fitar da sakamakon jarabawar kammala sakandare ta bana.
Babban jami’I kuma magatakardar hukumar, Ibrahim Dantani Wushishi, wanda ya bayyana hakan a Minna, babban birnin jihar Neja, ya shawarci wadanda abin ya shafa da su duba shafin hukumar jarabawar domin samun sakamakonsu.
Dantani Wushishi ya ce dalibai dubu 727 da 864 da ke wakiltar kashi 60.74 cikin 100 na adadin dalibai miliyan 1 da dubu 198 da 412 da suka zana jarrabawar, sun samu nasara a darussa biyar zuwa sama, da suka hada da Ingilishi da Lissafi.
Magatakardar, wanda ke bayyana sakamakon hukumar jarrabawar a karon farko a matsayinsa na cikakken shugaban hukumar, ya bayyana sakamakon a matsayin babban nasara.
Da ya juya kan batun satar amsa, Dantani Wushishi ya bayyana cewa, dalibai dubu 13 da 594 ne suka aikata laifukan satar amsa a bana, wadanda su ka kai kashi 0.13 cikin 100.