NDLEA ta lalata hodar iblis ta N194B

44

Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa NDLEA, ta lalata tan 1.8 na hodar iblis da kundinta ya kai N194Bn da jami’anta suka kwato daga wani dakin ajiyar kaya da ke Legas a makon jiya.

Kakakin hukumar, Femi Babafemi, a wata sanarwa da ya fitar a yau, ya tunatar da cewa hukumar ta NDLEA ta gudanar da wani samame na hadin gwiwa tare da leken asiri wanda ya dauki tsawon kwanaki biyu a makon da ya gabata, inda suka kai hari a wani boyayyen dakin ajiyar kaya da ke Legas inda aka gano tan 1.8 na hodar iblis tare da kama wasu mutane biyar da suka hada da wani dan kasar Jamaica.

Bayan kwace hodar, wanda shi ne mafi girma a tarihin hukumar, an samu amincewar babbar kotun tarayya da ke Legas don lalata kayayyakin jama’a.

A cewarsa, daga cikin tan 1.8 da aka kama, za a lalata dauri dubu 1 da 828 na hodar iblis ta hanyar konawa, yayin da sauran za a ajiye domin gurfanar da wadanda ake zargin da aka kawo su shaida da kuma sanya hannu kan takardar shaidar lalatawa.

Ya yabawa abokan huldar hukumar na kasa da kasa da suka tallafa wajen kama masu safarar hodar Iblis da kuma sojojin Najeriya da suka bada gudunmawa yayin aikin kamen.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

three + ten =