Najeriya na shirin fuskantar karuwar ambaliya bayan an bude dam a Kamaru

113

Hukumar bayar da agajin gaggawa ta kasa NEMA, ta gudanar da wani taron gaggawa a jiya biyo bayan mummunar ambaliyar ruwa da ka iya ta’azzara bayan da makwabciyarta kasar Kamaru ta bude madatsar ruwa domin sakin ruwa da yayi yawa.

Tun fara damina a watan Yuli, akalla mutane 300 ne suka mutu, wasu fiye da dubu 100 kuma suka rasa muhallansu a fadin kasar.

Darakta Janar na NEMA, Mustapha Habib Ahmed, ya ce jihohi 13 na cikin hadari.

Ya ce illar ballewar madatsar ruwa ta Lagdo ta kasar Kamaru hade da ruwan sama mai karfi ka iya shafar wasu jihohi ciki har da yankin Neja Delta mai arzikin mai.

Mustapha Ahmed ya ce ruwan da aka sako ya kara dagula al’amura a kasarnan, domin manyan madatsun ruwa a Najeriya da suka hada da Kainji, Jebba da Shiroro, suma ana sa ran za su iya ballewa daga yanzu zuwa karshen watan Oktoba.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

5 × four =