Mutane 76 sun mutu a zanga-zangar Iran

55

Akalla masu zanga-zanga 76 ne jami’an tsaron Iran suka kashe a tsawon kwanaki 11 da aka kwashe ana tashe tashen hankula sakamakon mutuwar wata mata da aka tsare.

Kungiyar kare hakkin bil’adama ta Iran mai hedkwata a kasar Norway, ta zargi hukumomi da yin amfani da karfin tuwo da harsashi mai rai wajen murkushe masu zanga-zanga.

Kafofin yada labaran kasar sun ce adadin wadanda suka mutu ya kai 41, ciki har da jami’an tsaro da dama, tare da dora alhakin mutuwar kan masu tayar da tarzoma.

An kuma kama daruruwan mutane, 20 daga cikinsu ‘yan jarida ne.

Ofishin kare hakkin bil adama na Majalisar Dinkin Duniya ya kuma ce ya damu matuka da yadda hukumomin kasar suka mayar da martani da tashin hankali, ya kuma bukace su da su mutunta ‘yancin gudanar da zanga-zangar cikin lumana.

Tun bayan jana’izar Mahsa Amini a ranar 17 ga watan Satumba, zanga-zangar adawa da gwamnati ta bazu zuwa birane da garuruwa sama da 80 a fadin kasar ta Iran.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

3 − 1 =