MDD tace zargin cin zarafin Musulman Uyghur a China gaskiya ne

35

Majalisar Dinkin Duniya ta zargi China da take hakkin dan adam a wani rahoto da aka dade ana jira kan zargin cin zarafi a lardin Xinjiang.

China ta bukaci Majalisar Dinkin Duniya da kada ta fitar da rahoton, inda ta kira shi a matsayin shirme da kasashen yamma suka shirya.

Rahoton ya yi la’akari da ikirarin cin zarafi da ake yi wa Musulman Uygur da wasu kabilu marasa rinjaye, abin da China ta musanta.

Sai dai masu binciken sun ce sun samu kwararan hujjoji na azabtarwa da ya kai ga cin zarafin bil’adama.

An fitar da rahoton ne a ranar karshe da Michelle Bachelet ke aiki bayan shekaru hudu a matsayin babbar kwamishiniyar kare hakkin dan adam ta Majalisar Dinkin Duniya.

Zargin cin zarafi da ake yiwa ‘yan Uygur ne ya mamaye wa’adin mulkin ta.

Rahoton tawagarta ya zargi kasar China da yin amfani da dokokin tsaron kasa marasa tushe don tauye hakkin tsiraru da assasa tsarin tsare mutane ba bisa ka’ida ba.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

three − 1 =