Kotu ta yankewa matasa hukuncin daurin rai da rai a Jigawa

149

Wata babbar kotun jihar Jigawa dake a garin Birnin Kudu ta yanke wa wani matashi mai suna Umar Danladi dan shekara 23 dan asalin Sabuwar Gwaram hukuncin daurin rai da rai bisa samunsa da laifin aikata fyade.

Kazalika, kotun ta zartar da irin wannan hukunci kan wani mai suna Abdussalam Saleh na kauyen Rafawa a karamar hukumar Dutse da Auwal Yunusa na Kafin Fulani a karamar hukumar Gwaram bisa aikata irin wannan laifin.

Da yake yanke hukunci a kan mutane ukun da aka gurfanar a gabansa, alkalin kotun, Mai shari’a Musa Ubale, ya ce kotun ta gamsu ba tare da wata shakka ba cewa wadanda aka yanke wa hukuncin sun aikata laifin da za a hukunta su a karkashin sashe na uku na kundin manyan laifuffuka na Penal code.

Mai shari’a Musa Ubale, a hukuncin da ya yanke, ya ce shaidun mai gabatar da kara sun mika wa kotu gamsassun hujjoji a kan wadanda ake tuhumar, domin tabbatar da sun aikata laifin, daga bisani kuma ya yanke musu hukuncin daurin rai da rai a karkashin sashe na uku na kundin manyan laifuffuka.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

5 × 2 =