Gwamnoni sun yi watsi da shirin gwamnatin tarayya na sayar da kamfanonin lantarki

28

Kungiyar Gwamnonin Najeriya a jiya ta yi adawa da kudirin Gwamnatin Tarayya na sayar da kamfanonin samar da wutar lantarki na kasa.

Kamfanonin samar da wutar lantarkin da gwamnatin tarayya ke shirin sayarwa sune na Benin, da na Calabar, da na Geregu, da na Olorunsogo da kuma na Omotosho.

Shugaban kungiyar gwamnonin Najeriya mai barin gado, kuma gwamnan jihar Ekiti, Kayode Fayemi, wanda ya yi jawabi a Abuja jiya bayan taron kungiyar, ya ce sun soki shirin sayarwar saboda ba a shigar da dukkan masu ruwa da tsaki ba.

Kungiyar ta kuma shawarci Gwamnatin Tarayya da ta daina hukunta Kungiyar Malaman Jami’o’i da ke yajin aiki.

Ta ce kamata ya yi gwamnati ta warware matsalolin da ake ta kika-kika akai domin moriyar daliban da ma Najeriya bakidaya.

Tun da farko dai shugaban kasa Muhammadu Buhari wanda mataimakinsa Yemi Osinbajo ya wakilta ya kaddamar da wani katafaren ofishin kungiyar gwamnonin Najeriya na biliyoyin naira a Maitama Abuja.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

twenty − one =