Gwamnatin Kaduna ta hana zanga-zanga kan titin Kaduna-Abuja

37

Gwamnatin jihar Kaduna a jiya ta ce ba za ta lamunci duk wani yunkurin wani mutum ko wata kungiya ba na toshe hanyar Kaduna zuwa Abuja da sunan zanga-zanga.

Kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na jihar Samuel Aruwan ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a Kaduna, inda ya ce ba za a amince da matakin ba wanda wani share fage ne na karya doka da oda.

A cewar sanarwar, da wannan umarni, an shawarci daidaikun mutane ko kungiyoyin da ke shirin takaita zirga-zirgar ‘yan kasa akan titin da su daina domin zaman lafiyar jama’a.

Sanarwar ta shawarci ‘yan kasar da su guji shiga irin wadannan zanga-zanga musamman wadanda za su yi tasiri ga al’amuran zamantakewa da tattalin arziki na sauran ‘yan kasar, ko kuma jefa rayuka cikin hatsarin da ba dole ba.

Don haka kwamishinan ya ce ya kamata daidaikun mutane da kungiyoyi su lura da shawarwarin da aka ba su, su nesanta kan su daga titin.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

10 + 4 =