Gwamnatin Jigawa za ta raba naira biliyan 1 da miliyan 700

149
Gwamnan Jihar Jigawa Muhammadu Badaru

Gwamnatin jihar Jigawa a jiya ta bayyana shirin fara rabon kudi naira miliyan dubu 1 da miliyan 700 ga mazauna karkara a matsayin tallafi kyauta ga talakawa da masu kakana da matsakaitan masana’antu.

Kwamishinan kudi da tsare-tsare na jihar Alhaji Ibrahim Umar ne ya bayyana hakan ga manema labarai a Dutse babban birnin jihar.

Kamfanin Dillancin Labarai na kasa ya bayar da rahoton cewa za a raba kudaden ne a karkashin shirin Gwamnatin Tarayya na farfadowa bayan annobar corona da karfafa tattalin arziki.

Kwamishinan ya ce an tsara shirin ne a matsayin sakamakon kokarin jihar yayin annobar corona wanda babban bankin duniya ya kaddamar domin taimakawa talakawan Najeriya da annobar corona ta shafa.

Ya ce tuni Bankin Duniya ya fitar da zunzurutun kudi har naira miliyan 700 domin fara shirin a jihar Jigawa kamar yadda ya kamata.

Sharhi 1

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

twelve − 5 =