Gwamnatin Jigawa za ta gina asibitin ƙashi

288
Gwamnan Jihar Jigawa Badaru Abubakar

Ma’aikatar lafiya ta jihar Jigawa ta yi bikin bude bada tayin kwangila na gina asibitin ƙashi na garin Gumel da wasu gine-gine a sabuwar makarantar koyon aikin jinya da ungozoma ta Babura da kuma wasu ayyuka a manyan asibitocin Gagarawa da Gwiwa da kuma Kiri-Kasamma.

A jawabinsa, babban sakataren ma’aikatar lafiya ta jiha Dokta Salisu Mu’azu yace ayyukan cigaba ne a kashi na uku na ayyukan.

Ya kara da cewa, aikin na daga cikin alƙawuran da gwamnati mai ci ta yi na inganta harkokin lafiya a jihar nan, inda yayi kira ga kamfanonin da zasu yi nasara dasu gudanar da aiki mai ingancin.

A nasa tsokacin, wakilin hukumar tantance ayyukan kwangila ta jiha, Alhaji Ahmed Isah, ya yabawa hukumar lafiya ta jiha, tare da yin kira ga yan kwangilar dasu kiyaye da ka’idojin aiki da kuma gudanar da ayyuka masu inganci.

Wakilan kamfanonin kwangilar sun sha alwashin gudanar da ayyuka masu kyau kamar ya kamata.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

one × 3 =