
Gwamnatin tarayya tace ta kammala ta dukkanin shirye-shiryen raba akalla tan dubu 12 na hatsi ga mabukata domin rage radadin hauhawar farashin kayan abinci.
Hakan ya fito ne ta bakin daraktan janar na hukumar agajin gaggawa ta kasa (NEMA), Mustapha Habi Ahmed, lokacin da ya ziyarci jihar Jigawa.
Darakta Janar yace shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da raba hatsin daga rumbunan adana hatsi na kasa.
Mustapha Habib yace hakan hanya ce ta dakile illar hauhawar farashin kayan masarufi da tsadar rayuwa sanadiyyar matsin tattalin arzikin duniya.
Ya kara da cewa rabon hatsin karamci ne na shugaban kasa Muhammadu Buhari domin rage radadin rayuwa ga wadanda iftila’in ambaliyar ruwa ta shafa a jihar Jigawa.
Yayi bayanin cewa tan dubu 12 na hatsin ya hada da masara da dawa da kuma gero.