Gwamna Zulum ya bada umarnin daukar ma’aikatan lafiya

61

Gwamna Babagana Zulum na jihar Borno ya ba da umarnin daukar ma’aikatan lafiya 30 cikin gaggawa da suka hada da likitoci da ma’aikatan jinya da ungozoma da masu hada magunguna da kuma kwararrun dakin gwaje-gwaje a babban asibitin garin Bama.

Karamar hukumar Bama dai na daya daga cikin yankunan da ‘yan tada kayar baya suka raba mutane da gidajensu, inda a yanzu haka jama’arsu ke komawa saboda ingancin tsaro.

Umurnin na kunshe ne a cikin wata sanarwa a yau ta hannun mai ba wa gwamnan shawara na musamman kan harkokin sadarwa da dabaru, Isa Gusau.

Babagana Zulum ya ziyarci asibitin a jiya inda ya gana da mahukuntan asibitin da sauran manyan jami’an ma’aikatar lafiya ta jihar domin gano kalubalen da asibitin ke fuskanta.

Ya nuna damuwarsa cewa babban asibitin yana da likitoci biyu ne kacal da ma’aikatan jinya da ungozoma guda 10.

Babagana Zulum ya kuma amince da sakin karin magunguna ga asibitin da kuma gyara gidajen ma’aikatan da aka yi watsi da su.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

6 − 5 =