Buhari ya kafa kwamitin da zai duba bukatun ASUU

53

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kafa wani kwamiti da zai duba bukatun kungiyar malaman jami’o’i ta kasa (ASUU).

Kungiyar ta tsunduma yajin aiki tun watan Fabrairu kuma gwamnatin tarayya ta yi amfani da kudirin babu aiki, babu biya, inda ta dage cewa ba za ta biya malaman albashin na tsawon lokacin da suka daina aiki ba.

Malaman sun yi watsi da hakan inda yajin aikin ya dore.

Sai dai a wani taro yau tare da shugabannin da mataimakan shugabannin jami’o’i na kasa a Abuja, Ministan Ilimi, Malam Adamu Adamu, ya bayyana cewa gwamnatin tarayya ta kafa kwamitin da zai sake duba batun.

Adamu Adamu ya ce kwamitin ya kunshi shugabannin jami’o’i hudu da mataimakansu hudu, yayin da shi ne shugaba.

Ya ce kwamitin zai duba karin bukatun ASUU musamman wuraren da ba a cimma matsaya ba.

Ministan ya ce zai yi wa shugaban kasa Muhammadu Buhari bayanin sakamakon taron.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

two × 4 =