Buhari ya kaddamar da majalisar sauyin yanayi ta kasa

40

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya bukaci majalisar sauyin yanayi ta kasa da ta samar da kudirorin da ake bukata domin cimma manufofin cigaban bishiyoyi da na tattalin arziki mai dorewa a Najeriya.

Shugaban kasar ya bayar da umarnin a yau yayin da yake kaddamar da majalisar gabannin fara zaman majalisar zartarwa ta kasa a fadar shugaban kasa dake Abuja.

Shugaban kasar yace kaddamar da majalisar ya aza harhasashin fara aiwatar da dokar sauyin yanayi ta shekarar 2021 tare da bude sabon shafin magance matsalolin sauyin yanayi a kasarnan.

Ya kuma bukaci babban lauyan tarayya kuma ministan shari’ah tare da hadin gwiwar ministan muhalli da su samar da gyare-gyaren da ake bukata domin magance kalubalen fara amfani da dokar.

Da yake tsokaci akan rayukan da dukiyoyin da aka rasa sanadiyyar ambaliyar ruwa a sassan kasarnan da dama da kuma kasashen Pakistan da Bangladesh tare da wasu sassan Gabashi da Kudancin Afrika, Shugaba Buhari ya bayyana sauyin yanayi a matsayin babban kalubalen da ke tunkarar bil’adama.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

fourteen + 6 =